BH ta kashe wani babban sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar
Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, tare da
wasu sojojin hudu, lokacin da suka dakile wani
harin mayakan Boko Haram a kan barikin sojin
kasar na 119 dake Mallam Fatori, jihar Borno.
Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, shi ne
kwamandan runduna ta 272 mai kula da tankokin
yaki.
Saboda jarumtarsa ne, a 2015 a Gamboru Ngala,
babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar
Janar Tukur Buratai ya yi mushi karin girma daga
Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai
shekarun samun karin girman.
Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin kasa
ta kasar, Kanar Sani Uman Kukasheka, ya ce
sojojin sun kashe mayakan Boko Haram din
goma sha hudu a lokacin artabun.
Ya ce wasu sojojin hudu kuma sun samu raunuka
a harin wanda mayakan kungiyar suka kai a
daren Juma'a.
Kanar Kukasheka ya ce cikin makaman da
sojojin suka kwace daga wurin mayakan sun
hada da babbar bindiga samfurin GPMG, da
AK-47 guda bakwai da kuma albarusai da dama.
Kakakin sojin ya kuma ce ana ci gaba da aikin
kakkabe mayakan Boko Haram din daga yankin.
A 'yan kwanakin nan dai, 'yan bindiga da ake gani
mayakan Boko Haram ne sun yi ta yunkurin kai
hare-hare a sassan jihar Borno da dama.
Ko a karshen watan Oktoba, sojojin Najeriyar
biyar da 'yan sintiri uku da dan kato da gora daya
sun rasa rayukansu lokacin da mayakan Boko
Haram din suka yi musu kwanton bauna a
kauyen Ugundiri dake karamar hukumar Damboa.
Sojoji sha tara kuma da dan kato da gora daya
sun sami raunuka a kwanton baunar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "BH ta kashe wani babban sojin Najeriya"

Post a Comment