Ba na fargabar zaman gidan kaso— Zuma

Shugaban Afirka ta Kudu Jocob wanda ake
alakantawa da zarge-zargen cin hanci da
rashawa, ya ce baya fargabar zaman gidan yari,
saboda shekaru goman da ya shafe a kurkuku
lokacin da yake mai fafutukar yaki da mulkin
wariyar launin fata.
Wannan ne karo na farko da shugaban ya mayar
da martani a bainar jama'a, tun bayan da wani
binciken cin hanci, ya bada shawarar a binciki
shugaban da wasu manyan jami'an gwamnati
akan ko sun yi wata hulda wacce bata dace ba
da wasu hanshakan 'yan kasuwa 'yan kasar
India.
Mista Zuma ya shaida wa dubban magoya
bayansa a lardin Kwa-Zulu Natal, cewa lauyoyi
da kotuna na kokarin tsawaita muhawara ta
demukradiya.
A cikin mako mai zuwa ne ake gani majalisar
dokokin kasar za ta gabatar da kudurin rashin
bashi goyon baya, koda yake a baya, ya tsallake
kudurori biyu na janye goyon bayan da majalisar
ke bashi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ba na fargabar zaman gidan kaso— Zuma"

Post a Comment