Donald Trump ya kama hanyar lashe zaben Amurka

Dan takarar jam'aiyyar Republican Donald Trump
ya shiga gaban Hillary Clinton a fafutukar lashe
muhimman jihohi domin zamowa shugaban
Amurka.
Gidan talabijin na ABC ya yi hasashen cewa tuni
ya lashe Florida, Ohio da North Carolina, yayin da
Clinton ta jam'iyyar Democrat ta lashe Virginia.
Ana kan-kan-kan a jihar Michigan, wacce rabon
da Republican ta lashe tun shekarar 1988.
Kasuwannin hannayen jari sun fadi tun bayan da
alamu suka fara nuna cewa Misis Clinton na
fuskantar koma baya.
Har ila yau ana sa ran jam'iyyar Republican za ta
rike rinjayen da ta ke da shi a majalisar wakilan
kasar.
Ana bukatar dan takara ya samu wakilai 270
daga cikin 538 (wato electoral college) domin
samun nasara.
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta BBC ta nuna cewa
Clinton na gaban Trump da maki hudu kacal.
Da sanyin safiya misalin karfe 06:00 ne aka fara
kada kuri'a a Gabashin kasar, sai dai tuni wasu
kauyuka a jihar New Hampshire sun riga sun
kada kuri'unsu.
Duka Misis Clinton da Mista Trump sun kada
kuri'unsu a mazabu daban-daban a birnin New
York.
An samu dogayen layuka a wasu jihohin, abin da
ke nuna yadda jama'a suka fito sosai.
Wasu wuraren kada kuri'ar sun samu matsalolin
na'ura, abin da ya haifar da jinkiri.
Duka 'yan takarar sun yi gangamin yakin neman
zabe a jihohin North Carolina da Pennsylvania da
kuma Michigan, inda nan ne takarar ta fi zafi.
Sai dai tuni Amurkawa miliyan 46 suka jefa
kuri'unsu a jihohin da suka bude rumfunan
zabensu kwanakki gabanin wannan ranar ta
zaben gama-gari.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan asalin Latin
Amurka masu amfani da yaren Spaniya, wadanda
ke goyon bayan Hillary Clinto, sun fito sosai.
Hillary Clinton da Donald Trump sun zagaye
kasar domin neman kuri'un jama'a a 'yan
kwanakin da suka gabata.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Donald Trump ya kama hanyar lashe zaben Amurka"

Post a Comment