Donald Trump ya lashe zaben Amurka

Dan takarar Shugabancin Amurka na jam'iyyar
Republican, Donald Trump, ya lashe zaben kasar
da aka yi ranar Talata.
Mista Trump ya lashe zaben ne bayan da ya
samu nasarar cinye kujerun wakilai sama da 270
a jihohi 50, a inda ya kayar da abokiyar
hamayyarsa Hillary Clinton.
Trump, wanda yanzu haka yake gabatar da
jawabin amincewa da yin nasara, ya ce Clinton
ta kira wo shi a wayar tarho inda ta taya shi
muranr lashe zaben.
Dan takarar jam'iyyar Republican, Donald Trump
ya lashe kuri'un jihohin da ke Yammacin kasar na
tsakiya da kuma kudanci.
Ita kuma 'yar takarar Democrat, Hillary Clinton ta
share jihohin Arewa Maso gabashin kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Donald Trump ya lashe zaben Amurka"

Post a Comment