Kwayar cutar kwanputa ta 'kashe' shugaban Facebook

Wata cutar da ake yadawa a kwamputa, wacce
ta samu shafin Facebook, ta sa shafin ya sanar
da mutuwar mutane da dama, ciki har da mai
Mark Zuckerberg, mai kamfanin na Facebook.
Cutar dai ta sa shafin na sada zumunta ya
wallafa wasu bayanai a shafukan Facebook na
wasu mutane, wadanda za su nuna wa duk
mutumin da ya ziyarci shafukan cewa mutanen
fa sun mutu.
Hakan ya sa mutanen sun rika wallafa sakonnin
da ke nuna cewa ba su mutu ba domin kawar da
tashin hankalin da abokansu ka iya fada wa a
ciki.
Kakakin kamfanin na Facebook ya bayar da
hakuri a kan wannan gagarumin kuskure suka yi.
Ya kara da cewa,"Wannan ba karamin kuskure ba
ne, amma dai mun gyara shi. Muna matukar
bayar da hakuri a kan hakan."
A cewarsa, ana wallafa irin wadannan bayanai ne
kawai a shafukan mutanen da suka mutu ta
yadda abokansu da ke da rai za su rika tunawa
da su, amma sai ga shi an ce mai kamfanin na
Facebook na cikin wadanda suka rasu.
Sakon da aka wallafa a shafin Mr Zuckerberg ya
ce "Muna fatan mutanen da ke kaunar Mark za
su kwantar da hankalinsu sannan su rika tunawa
da abubuwan na bajinta da ya yi a lokacin da
yake raye."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kwayar cutar kwanputa ta 'kashe' shugaban Facebook"

Post a Comment