Mexico ta casa Amurka

Kasar Mexico ta doke Amurka da ci 2-1 a wasan
neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya.
Kyaftin din Mexico Rafael Marquez ne ya zuwa
kwallon da ta ba su nasara a minti na 89.
Wasan wanda aka yi a Columbus, jihar Ohio ya
zo da wani batu domin kuwa an yi shi ne bayan
Donald Trump, mutumin da ya sha alwashin gina
katanga tsakanin Amurka da Mexico, ya lashe
zabe.
Mexico ta ci kwallonta ta farko ne ta Miguel
Layun, kodayake dan wasan Bobby Wood ya
farke bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Nasarar da Mexico ta yi ta kawo karshen kashin
da suka sha sau hudu a Ohio - jihar da take da
muhimmanci, kuma wacce Trump ya ci zaben ta
- domin kuwa tun shekarar 2001 suke kokarin cin
wasa a jihar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mexico ta casa Amurka"

Post a Comment