NATO ta gargadi Donald Trump

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO, ya
gargadi zababben shugaban Amurka Donald
Trump cewa matakin da ya ke shirin dauka kan
dangantakar da ke tsakanin Amurka da tarayyar
turai bai dace ba.
Mista Jens Stoltenberg ya yi wannan kalami ne a
jaridar Observer ta Birtaniya, inda ya kara da
cewa kasashen yammacin duniya na fuskantar
kalubalen tsaro da aka dade ba a ga irin shi ba.
A lokacin yakin neman zabe, Mista Trump ya ce
idan ya yi nasarar zama shugaban kasa zai sake
nazari kan yiwuwar taimakawa kasashe kawayen
Amurka da aka kai wa hari idan har ba ta biya
abubuwan da suka zama hakki kasar ta biya ba a
cikin kawancen NATO.
An kuma ambato mai magana da yawun shugaba
Vladimir Putin na Rasha na cewa da Mista
Trump zai matsawa NATO lambar janye dakarun
su daga iyakar kasar Rasha, kuma tabbas za su
kulla alaka mai aminci tsakanin su da Amurka.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "NATO ta gargadi Donald Trump"

Post a Comment