Nigeria ta hada maki uku a kan Algeria a ranar Asabar

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta doke ta
Aljeria da ci 3-1 a wasan shiga gasar cin kofin
duniya da suka fafata a filin wasa na Uyo da ke
Akwa Ibom a ranar Asabar.
Nigeria ta fara cin kwallo ta hannun Victor
Moses a minti na 26 da fara tamaula, sannan
kyaftin din Super Eagles, John Mikel Obi, ya ci ta
biyu daf da za a je hutu.
Bayan da aka dawo ne Algeria ta farke kwallo
daya ta hannun Nabil Bentaleb, sai dai daf da za
a tashi Victor Moses ya ci wa Nigeria kwallo na
uku kuma na biyu da ya ci a fafatawar.
Daya wasan na rukuni na biyu tsakanin Kamaru
da Zambiya tashi suka yi kunnen doki 1-1.
Da wannan sakamakon Nigeria ce ta daya a kan
teburi da maki shida, sai Kamaru ta biyu da maki
biyu, yayin da Zambia da Algeria ke da maki
daya-daya.
Nigeria za ta karbi bakuncin Kamaru a ranar 27
ga watan Agustan 2017, inda a ranar ne Algeria
za ta ziyarci Zambia.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria ta hada maki uku a kan Algeria a ranar Asabar"

Post a Comment