Ondo: An amince Jegede ya zama dan takara daya tilo

– Peoples Democratic Party (PDP) na ci
gaba da zama cikin rudani game da zaben
gwamnan jihar Ondo
– Duk da yake kotun daukaka kara taki
yanke hukunci kan Jimoh Ibrahim, PDP ta
fadi matakin da ta dauka

Eyitayo Jegede

Mai yiwuwa Peoples Democratic Party (PDP)
tayi watsi da kotun daukaka kara wadda taki
yanke hukunci kan karar da aka kai dan
kasuwa Jimoh Ibrahim, wani dan takara na
wani bangaren jam’iyyar a zaben gwamnan
jihar Ondo wanda za’a yi.
Za’a yi zaben wajen karshen Nuwamba,kuma
ga alama PDP bata gamsu ba cewa ‘yan
satuttuka kafin zaben, jam’iyyar mai alamar
lema ta rabu gida biyu mai ‘yan takara biyu.
Bangaren Ahmed Makarfi na PDP ya zabi
Eyitayo Jegede, wani tsohon kwamishina a
jihar, amma mai shari’a Okon Abang ya ba
Ibrahim gaskiya.
Ranar Talata 1 ga Nuwamba, kotun daukaka
kara taki ta yanke hukunci kan maganar da
Jegede ya kawo,mamadin haka sai ta mayar
da takardun shari’ar.
Amma ‘yan awowi bayan kotun daukaka
karar ta gama zamanta,duka shuwagabanni
36 na jiha na PDP sun yi taro da
shuwagabannin jam’iyya na kasa suka bada
goyon bayansu ga Jegede a matsayin dan
takara na ainihi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ondo: An amince Jegede ya zama dan takara daya tilo"

Post a Comment