Legia da Real Madrid sun tashi wasa 3-3

Legia Warsaw da Real Madrid sun tashi wasa
3-3 a gasar cin Kofin Zakarun Turai da suka
fafata a ranar Laraba.
Gareth Bale ne ya fara ci wa Madrid kwallo a
mintin farko da fara wasa, kuma Kareem
Benzema ya kara ta biyu saura minti 10 a je
hutun rabin lokaci.
Saura minti biyar a je hutu ne, Legia ta zare
kwallon farko ta hannun Odjidja-Ofoe da kuma ta
biyu ta hannun Radovic, sannan ta ci ta uku
saura minti bakwai a tashi daga karawar ta
hannun Moulin.
Sai dai kuma ya rage saura minti biyar alkalin
wasa ya tashi fafatawar Madrid ta farke ta
hannun Kovacic.
Da wannan sakamakon Real Madrid tana mataki
na daya a kan teburin rukuni na shida, yayain da
Legia ce ta karshe da maki daya.
Borussia Dortmund wanda ta ci Sporting 1-0 a
ranar ta Laraba ce ke matsayi na daya da maki
10, ita kuwa Sporting tana da maki uku a mataki
na uku.
Ga sauran sakamakon wasannin da aka yi:
Monaco 3 vs CSKA 0
Tottenham 0 vs Bayer Levkn 1
Bor Dortmd 1 vs Sporting 0
FC Copenhagen 0 vs Leicesterm 0
FC Porto 1 vs Club Brugge 0
Juventus 1 vs Lyon 1
Sevilla 4 vs Dinamo Zagreb 0

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Legia da Real Madrid sun tashi wasa 3-3"

Post a Comment