Rundunar soji sun saki mutane 1271 da ake wa zargi

Rundunar sojin Najeriya sun sake wadanda
aka tsare guda 1271 a ake zargi da ewan
yan boko haram ne
– An sake musamman mata da a yara ,
dakkansu ana basu abinci sau 3 a rana
Wasu daga cikin sun gwammace su kasance
da mu kada su koma sansanin yan gudun
hijira.
Nigerian soldiers
Rundunar sojin Najeriya sun bada rahoton
cewa an sake wadanda aka damke bayan an
tabbatar da cewa basuda wata alaka da
Boko Haram.
Kwamandan sashe na 7 da ke Maiduguri,
Brigadir-General Victor Ezugwu,ne ya
bayyana haka a wata taron hada yaran da
suke da alaka da sojoji ko kungiyoyin yan
bindiga a ranan litinin ,7 ga watan nuwamba.
Brigadir-General Victor Ezugwu,ya jaddada
cewa mafi akasarin su mata da yara ne
kuma an kare musu hakkinsu.
Yace: “Muna kokari a koda yaushe wajen
gaggauta gudanar da bincike kuma muna
sakin wadanda muka samu basu da laifi.”
Game da cewar Brigadir-Janar Victor
Ezugwu, ana ciyar da yaran sau 3 a rana
kuma da koshin lafiya.
“Koda yaushe muna basu nama ko kifi a
kowani abinci da kuma kayan itace a ranan
lahadi. Kana wasu daga cikinsu ma basu son
sun gammace su tsaya da mu fiye da komawa
sansanin yan gudun hijra.”

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Rundunar soji sun saki mutane 1271 da ake wa zargi"

Post a Comment