Soyinka ya ce zai bar Amurka ranar da Trump ya karbi mulki

Shahararren marubucin nan na Nigeria Wole
Soyinka ya ce zai bar Amurka a ranar da aka
rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban
kasa.
A wani martani da ya mayar na sakonnin imel da
aka aike masa, Soyinka ya ce a ranar 20 ga
watan Janairu na shekarar 2017, "ku kalli ficewa
ta daga Amurka".
Mujallar Newsweek da ke Amurka ta ce zai
kasance a kasar har sai Trump ya sha rantsuwa.
Ta kara da cewa, "An ambato Soyinka yana cewa
"me ya sa ba za a jira har sai Trump ya karbi
ragamar mulki ba?
"Ina aikace-aikacena na yau da kullum, amma
kuma ba zan kara yin wasu ayyukan ba. A halin
yanzu dai mu tsaya a kan hakan."
A makon da ya gabata ne dai Mista Soyinka ya
yi alkawarin cewa zai yaga takardar izinin
zamansa a Amurka, wato Green card idan Mista
Trump ya yi nasarar zabe.
Kalamansa dai sun bayyana ne a wata
tattaunawar bidiyo da ya yi da dalibai wadda aka
nada a Jami'ar Oxford da ke Biritaniya.
Wole Soyinka dai ya yi hakan ne a matsayin wani
martani ga tsauraran matakan da Donald Trump
yake so ya dauka kan shiga da fita Amurka.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Soyinka ya ce zai bar Amurka ranar da Trump ya karbi mulki"

Post a Comment