Ivory Coast ta hana sayar da giya a leda

Kasar Ivory Coast ta hana sayar da barasar da
ake durawa a cikin leda kamar yadda mai
magana da yawun gwamnatin kasar, Bruno Kone
ya ce.
Sananniyar giyar ledar na zuwa ne a samfuri
daban-daban kamar giyar rum, vodka ko kuma
wasu da ake sayarwa daga farashin sefa 200
zuwa sefa 1,000.
Mista Kone ya ce gwamanti ta hana sayar da
barasar ledar ne bisa dalilian lafiya, da kuma
hana mutane kasancewa 'yan maye.
Mutane sun mayar da martani da dama a kan
sanarwar, wacce kamfanin yada labarai na kasa
ya fitar a shafinsa na Twitter.
'Yan kasar suna shakkun ko da gaske gwamnati
za ta aiwatar da hukuncin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ivory Coast ta hana sayar da giya a leda"

Post a Comment