Dalilai biyar da suka sa Trump ya yi nasara

Donald Trump ya bayar da mamaki sosai tun
daga farkon lokacin da ya shiga takarar neman
shugabancin Amurka shekara daya da ta wuce.
Mutane kalilan ne suka yi tsammanin zai iya yin
takarar, amma kuma sai ga shi ya yi. Ba su yi
zaton zai yi nasara a zaben ba, sai kuma ya yi.
Sun ce ba zai ci zaben fitar da gwani na
jam'iyyar Republican ba, amma ya lashe zaben.
Da karshe sai suka ce babu yadda zai iya
fafatawa a zaben ballantana ma ya yi nasara a
babban zaben.
Yanzu dai Donald Trump shi ne zababben
shugaban kasar Amurka.
Ga abubuwa biyar da suka sanya ya yi ba-zata,
har ya lashe zaben na shugaban kasa:
Farar-fatar Amurka sun fi son Trump
Kamar a mafarki, manyan jihohi daya bayan daya
irin su Ohio, Florida da kuma North Carolina sun
zabi Mista Trump.
Hakan ya sa Misis Clinton ta yi faduwar bakar-
tasa.
Fatan 'yan jam'iyyar Democrat na karshe shi ne
su yi nasara a jihohin tsakiyar yammacin kasar.
Su ne jihohin da jam'iyyar ta kwashe shekara da
shekaru tana cin zabe, saboda yawancin
mazaunansu bakar-fata ne da kuma farar-fata
ma'aikata.
Yawancin farar-fatar, musamman wadanda ba su
da ilimi - maza da mata - sun kauracewa
jam'iyyar.
Su kuwa masu kada kuri'a da ke karkara sun fito
kwansu-da-kwarkwata musamman ganin yadda
suke jin haushin cewa attajirai sun yi watsi da
su.
Kodayake jihohi irin su Virginia da Colorado sun
zabi Cliton, amma ta sha kaye a Wisconsin -
kuma hakan ya yi sanadin faduwarta.
Idan aka yi la'akari da yadda al'amura suka
gudana, za a iya cewa Misis Clinton za ta iya
cinye zaben California da New York saboda
yawan goyon bayan da take da shi a can, sai dai
ta sha mamaki a jihohi irin su Utah.
Guguwar Trump ta mamaye wadannan jihohin.
Yadda Donald Trump ya samu nasarar
zama shugaban kasa
Donald ba ya ganin kowa ga gashi
Mr Trump ya zagi fitaccen tsohon sojan nan da
ya yi wa Amurka yaki John McCain.
Ya yi fada da gidan talabijin na Fox News da
fitacciyar mai gabatar da shirin nan Megyn Kelly.
Ya nemi fada a lokacin da aka tambaye shi
dalilin da ya sa ya zolayi sarauniyar kyau 'yar
Hispania saboda tebarta.
Bai yi da-na-sani ba lokacin da aka fitar da wani
bidiyo da ke nuna shi yana neman yin lalata da
wasu mata.
Sau uku yana yin mummunar katobara a lokacin
muharawar da suka yi da abokiyar takararsa.
Amma duk da wadannan batutuwa, sai ga shi an
zabe shi.
Farin-shiga
Ya fafata da 'yan Democrat. Kazalika ya
kalubalancin masu ruwa da tsaki a jam'iyyarsa.
Kuma ya yi nasara a kansu.
Mr Trump ya yi wasu dabaru da suka karya lagon
abokan takararsa na zaben fitar da gwani na
Republican. Wasu daga cikin su, kamar Marco
Rubio, Ted Cruz, Chris Christie da Ben Carson,
sun bayar da kai bori ya hau.
Wadanda kuma ba su mika wuya ba, irin su Jeb
Bush da gwamna Ohio John Kasich, sun zama
'yan kallo.
Haka kuma sauran manyan 'yan jam'iyyar da ba
su goyi bayansa ba, kamar kakakin majalisar
wakilai Paul Ryan ba su da wani tasiri domin
Mista Trump ba ya bukatar taimakonsu a yanzu.
Hasalima, ana ganin ya ci zabe ne saboda ya ce
zai karya kashin bayansu.
Rawar da FBI ta taka
Da alama kuri'ar jin ra'ayoyin jama'ar da aka yi
ba ta yi amfani ba, musamman idan aka yi
la'akari da sakamakon zaben jihohin tsakiyar
yammacin kasar.
Ta fito fili cewa a lokacin da aka kusa yin zaben,
kuri'un sun nuna cewa 'yan takarar biyu suna
kankankan, kuma daga karshe an ga yadda Mr
Trump ya yi nasara.
Sai dai alamar yin nasararsa ta bayyana sosai ne
makonni biyu kafin zaben, kafin ma shugaban
hukumar bincike ta FBI James Comey ya sake
bude batun binciken sakonnin email din Hillary
Clinton.
A zahiri, kuri'ar jin ra'ayin jama ta nuna cewa
suna kankankan, amma farin-jinin Mr Trump ya
karu sosai ne tsakanin lokacin farko da FBI ta ce
za ta binciki Clinton da kuma lokaci na biyu da
ta sake tayar da maganar.
A lokacin ne Mista Trump ya karfafa irin goyon
bayan da yake da shi, kodayake shi kan sa
Comey bai tsira daga suka daga wajen Trump
ba.
Trump ya yarda da kansa
Mr Trump ya fafata ne a yakin neman zaben da
ba kasafai ake yin irinsa ba, kuma hakan ya ba
shi dama ta musamman.
Ya mayar da hankalinsa ne kan yadda zai ja
magoya bayansa a jiki, maimakon yin la'akari da
kuri'ar jin ra'ayin jama'a.
Ya ziyarci jihohi irin su Wisconsin da Michigan
wadanda masu fashin-baki suka ce ba zai iya
lashe wa ba.
Ya gudanar da manya-manyan tarukan yakin
neman zabe a madadin bi gida-gida yana neman
kuri'a.
Kudaden da Clinton ta kashe wajen yakin neman
zabe sun ninka nasa ba sau daya ba, kamar
yadda mutanen da suka yi takarar fitar da gwani
da shi a jam'iyyar Republican suka fi shi kashe
kudade.
Sai dai yana da wani siddabaru na jan hankalin
mutane ta hanyar kalamansa na kin jinin
mutanen.
A karshe dai, bukatarsa ta biya - kuma shi da
iyalinsa da kadan daga masu ba shi shawara - su
ne za su shiga fadar White House.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dalilai biyar da suka sa Trump ya yi nasara"

Post a Comment