Ta kwabewa Messi da kasar sa Argentina

Neymar da Philippe Coutinho kowannen su
ya zura kwallo guda a wasan da Brazil ta
doke Argentina da ci 3-0 a wasan neman
cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta
2018.
– ‘Yan wasan Argentina, cikin su har da
Lionel Messi sun yi kokarin yin tasiri a
wasan, sai dai Paulinho ya zura tasa
kwallon.
– Yanzu dai Argentina tana mataki na shida
a cikin tawaga 10 daga yammacin Amurka
da ke son shiga gasar cin kofin duniya,
kuma tuni hudu daga cikin su suka cancanci
shiga gasar.
Argentina tana da makin 16 a wasa 11 da ta
buga, wato tana bayan Ecuador, wacce take
ta hudu da maki daya, kuma ita ce ta takwas
a bayan Brazil, wacce ke da maki 24.
A wani labarin kuma, Wani alkali a Spaniya
ya ce ya kamata a gabatar da Barcelona da
Neymar gaban kotu, kan zargin zamba, wata
guda bayan da aka janye karar da aka shigar
tun farko.
A ranar Litinin wata gidauniya mai suna DIS
ce ta bukaci a sake sauraren karar, inda ta
ce an yi mata cogen a lokacin da Neymar ya
koma Barcelona daga Santos a shekarar
2013.
Gidauniyar ce ke kula da hakkin dan kwallon
na Brazil a harkar sauya kungiya.
Zargin da Neymar da iyayensa suka karyata,
wanda daga bisani aka kuma kori karar tun a
cikin watan Yuni.
A cikin watan Satumba, babbar kotun
Spaniya karkashin Alkali Jose de la Mata ya
bayar da umarnin da a sake sauraren karar.
Dan wasan ya tsawaita zamansa a
Barcelona kan yarjejeniyar shekara biyar a
cikin watan Oktoba.
Tun a baya an umarci Barcelona ta biya
tarar kudi fam miliyan 4.7, saboda kokarin
kauce wa biyan haraji kan cinikin Neymar.
An bai wa masu shigar da kara na Spaniya
kwanaki 10 da su shirya gabatar da
Barcelona da Neymar gaban kuliya.
A wani labarin kuma Lionel Messi ya ci
kwallo ta 500 a Barcelona a ranar Lahadi a
wasan da suka doke Sevilla 2-1 a ranar
Lahadi a gasar La Liga wasan mako na 11
da suka yi.
Messi mai shekara 29, ya ci wa Barca
kwallaye 500 a wasanni 592 da ya buga
mata tamaula, ciki har da wasannin sada
zumunta.
Dan wasan ya fara ci wa Barcelona kwallo a
cikin watan Mayun 2005, a lokacin yana da
shekara 17.
Yanzu haka dan kwallon na Argentina ya bai
wa Paulino Alcantara tazarar kwallaye 105,
wanda ya rike matsayin dan wasan da ya fi
ci wa kungiyar kwallaye a shekarar 1912 da
1927.
A cikin watan Afirilu ya ci kwallo na 500 a
wasannin da ya buga wa kasarsa da
Barcelona a karawar da suka ci Valencia 2-1.
Messi ya zura kwallaye 320 a manyan
wasannin Spaniya da kuma 90 da ya ci a
gasar cin kofin zakarun Turai, sauran ya ci
su ne a Uefa Super Cup da gasar kofin
duniya ta zakarun nahiyoyi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ta kwabewa Messi da kasar sa Argentina"

Post a Comment