Tsagerun Neja Delta sun sake wata tabargazar

Kungiyar Tsagerun Najeriya da ake kira
Neja Delta Avengers sun dauki alhakin kai
hari tashar fitar da danyan man fetur din
kasar zuwa kasuwannin duniya mallakar
kamfanin Shell.
– Mai Magana da yawun kungiyar, ya sanar
ta kafar sadarwar twitter cewar, su suka
fasa bututun man.
Rahotanni sun tabbatar da fasa bututun
ranar talata, wanda ake ganin babbar koma
baya ne ga yunkurin gwamnatin kasar na
sasantawa da mutanen Yankin Neja Delta.
A jiya ne dai NAIJ.com ta ruwato cewa A
Najeriya, kamfanin mai na Shell, ya ce ya
rufe tashar samar da iskar gas ta Escravos
da ke yankin Neja Delta mai azrikin man
fetur.
Sanarwar na zuwa ne sakamakon zanga-
zangar da wasu mazauna yankin suka yi a
ranar Laraba.
A cikin wani sakon email da ya aikewa
manema labarai, kamfanin na Shell din ya ce
zai cigaba da ayyukansa a Escravos din idan
masu zanga-zangar sun watse.
Masu zanga zangar sun kwashe kwanaki
takwas suna gudanarwa, inda suka yi korafin
rashin ababem more rayuwa a yankin.
Mai karatu zai iya tunawa cewa a ranar
laraba ma dai Tsagerun nan na Neja Delta da
kewa kansu lakabi da Niger Delta Avengers
(NDA) sun dauki alhakin kai harin da yayi
sanadiyyar fasa wani bututun mai na Trsan
Forcados dake a cikin dazukan karamar
hukumar Warri ta kudu a jihar Delta.
Mai magana da yawun tsagerun na Niger
Delta Avengers (NDA) Mudoch Agbinibo ne
ya sanar da haka a cikin wani jerin sako da
ya wallafa a shafin sa na Tuwita mai adreshi
@agbiniboND a jiya Laraba inda yace
wannan yana zaman kashedi ne ga sauran
kamfunnan man kasar nan dake a yankin na
Neja Delta inda kuma ya jadda aniyar su ta
ci gaba da kai irin wadannan hare-haren a
dukkan bututun man dake a yankin nasu.
Wannan sabbin hare-haren dai suna zuwa ne
kimanin awanni 24 bayan wani bututun man
da wasu tsagerun da ba’asan ko suwaye ba
suka fasa a wani wurin daban duk dai a cikin
jihar ta Delta a sanyin safiyar jiya.
Kafin dai daukar alhakin kai harin da Niger
Delta Avengers (NDA) tayi, a safiyar yau
kamfanin jaridar Daily Post ta wallafa
rahoton cewa bututun man da aka fasa na
Trans Forcados yana fidda mai ne daga
kauyen Batan na jihar ta Delta.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Tsagerun Neja Delta sun sake wata tabargazar"

Post a Comment