Wani mutun ya auri macijiyar sa
Wani mutum ya auri macijiyar sa, bayan
dayayi tunanin matarsa data mutune ta
koma jikin macijiyar.
– A cewar rahoton, macijiyar da take da
tsawon takun kafa 10, mai suna kobra, yayi
hakan ne domin ya maye gurbin soyayyar da
yakema matar sa.
Mutumin da ba’a bayyana sunan saba, an dai
bayyana cewar ya samu karayar zuciyane
alokacin daya rasa matar tasa shekaru biyar
da suka wuce. Amman saidai kuma yana
yima macijiyar nasa kallon masoyiyar tasa,
kawai sai ya yanke shawaran cewar ya auri
macijiyar nasa kawai domin ya maye gurbin
matar nasa.
Yakan bata lokacinsa tare da katon
macijiyar.
Mutumin dai yayi imani da cewar mutane
sukan saba sosai tare da dabbobi, wannan
shiya kara masa kwarin gwiwa.
A hotunan dai zaku ga yadda mutumin yake
cin abinci da macijiyar tare kuma suyi wasa
tare sannan su kalli TV tare.
Wanda ya saki hotunan dai ya bayyana
cewar, mutumin bai rabuwa da macijiyar duk
inda zaije, ko bacci tare sukeyi, ko yaushe
suna tare.
Sanannen mutum ne wanda akafi sani da
mai maciji, kuma ansha gaya masa cewar
maciji abune mai hatsarin gaske, Amman
baiji ba.
Wa’annan hotunan dai sun nuna cewar bazai
rabu da wannan macijiyar ba.
Allah ya kyauta!
Gaskiya ne
ReplyDelete