Ban sanya ranar da zan yaga katin zama a Amurka ba - Soyinka

Shahararren marubucin nan na Nigeria Wole
Soyinka ya ce bai sanya ranar da yaga takardar
izinin zamansa a Amurka, wato Green card ba.
A wata sanarwa da ya fitar, Mista Soyinka ya yi
kakkausan suka ga masu mu'amala da shafukan
intanet da na sada zumunta, wadanda ya ce su
suka yi masa ƙage cewa ya ce zai bar Amurka a
ranar da aka rantsar da Donald Trump a
matsayin shugaban kasa.
Sanarwar ta kara da cewa, "Bari na yi kashedi ga
masu amfani da intanet: su sani cewa wataƙila
ba a ƙyamar kasarsu Trump kamar yadda ake
ƙyamar Najeriya wacce aka tilasta mana zama a
cikin ta.
"Ya kamata su koma makaranta ku nemi ilimi.
Halilci shi ne babbar matsalarku, domin shi yake
sanya wa kuna tsoma baki a sha'anin da bai
shafe ku ba."
Soyinka ya jaddada cewa zai yaga takardarsa ta
izinin zama a Amurka, yama mai cewa zai yi
hakan ne a lokacin da ya ga dama.
Shahararren marubucin dai ya gamu da sukar
masu amfani da shafukan sada zumunta ne tun
da aka ga bai bar yaga katin ba kamar yadda ya
yi alkawarin yi idan Donald Trump ya lashe zaben
shugaban Amurka.
Mako biyu da suka wuce ne dai Mista Soyinka ya
yi alkawarin cewa zai yaga takardar izinin
zamansa a Amurka, wato Green card idan Mista
Trump ya yi nasarar zabe.
Ya yi alkawarin ne a tattaunawar bidiyo da ya yi
da dalibai wadda aka nada a Jami'ar Oxford da
ke Biritaniya.
Wole Soyinka dai ya yi hakan ne a matsayin wani
martani ga tsauraran matakan da Donald Trump
yake so ya dauka kan shiga da fita Amurka.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ban sanya ranar da zan yaga katin zama a Amurka ba - Soyinka"

Post a Comment