Amurka: 'Yar gudun hijira ta zama wakiliya a majalisa

Wata 'yar asalin Somalia kuma 'yar gudun hijira
ta kafa tarihi a Amurka, inda ta zama 'yar
majalisar wakilan kasar.
Ta shai da wa BBC cewa yaki da tsangwamar
musulmai bakar fata da ake yi a Amurkar na
daga cikin abubuwan da zata fi bai wa fifiko.
An dai zabi Ilhan Omar mai shekaru 34, don ta
wakilci jihar Minnesota a majasalisar wakilai.
Kuma ta shaida wa Bola Munsoro ta sashen
turanci abubuwan da take so ta cimma a
matsayin ta na wakiliyar al'uma.
Ita dai Ilham ta na da shekaru 12 suka isa
Amurka ita da iyayen ta a matsayin 'yan gudun
hijira, kuma ta fara makaranta ne daga aji shida
na firamare.
Ta dai sha fuskantar tsangwama a wajen 'yan
uwanta dalibai, saboda rashin iya turancin
ingilishi.
Amma idan ta yi wa mahaifin ta korafi, ya kan
bata kwarin gwiwa da cewa ta dage da karatu,
matukar iya harshen ingilishi to za ta samu
sassaucin tsangwama daga abokanta.
Burin Ilham dai a yanzu bai wuce ganin ci gaban
'yan uwanta 'yan gudun hijira da suke zaune a
Amurka shekara da shekaru.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Amurka: 'Yar gudun hijira ta zama wakiliya a majalisa"

Post a Comment