Obama ya gana da Donald Trump a White House

Shugaban Amurka Barrack Obama ya tattauna da
sabon shugaban kasar da aka zaba na jamiyyar
Republican Donald Trump a fadar White House.
Shugaba Obama ya ce sun tabo batutuwa da
dama a tattaunawar da suka yi wadanda suka
hada da batun cikin gida da kuma manufofin
kasar kan kasashen waje.
Ya kara da cewa yana son Mr Trump da matarsa
su ji cewa sun sami kyakkyawar maraba inda ya
jaddadawa zababben shugaban kasar cewa za su
yi duk abinda za su iya yi domin taimaka masa
yin nasara.
Shi ma a nasa bangaren Mista Trump ya ce sun
tattauna kan batutuwa da dama wasu daga ciki
masu kyau ne yayin da wasu kuma masu
sarkakiya sosai.
Tun da farko da yake jawabi ranar Laraba bayan
da aka sanar da sakamakon zaben, Mista Donald
Trump, ya ce zai saka muradun Amurka gaba da
komai, amma zai yi adalci ga kasashen da ke da
sha'awar tafiya tare da Amurka.
Mista Trump ya lashe zaben ne bayan da ya
samu kujerun wakilai sama da 270 a jihohi 50, a
inda ya kayar da abokiyar hamayyarsa Hillary
Clinton.
Trump, wanda ya gabatar da jawabin amincewa
da yin nasara, ya ce Clinton ta kira shi ta wayar
tarho inda ta taya shi murnar lashe zaben.
A cewarsa, zai mayar da hankali wajen ganin ya
sake gina Amurka, yana mai cewa muradin kasar
su zai sanya farko a kan komai.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Obama ya gana da Donald Trump a White House"

Post a Comment