Amurkawa na zaben shugaban kasa na gaba

Masu zaben a kasar Amurka na ci gaba da
tururuwa zuwa rumfunan zabe domin zaben
shugaban kasar na gaba.
Ana fafatawa ne tsakanin 'yan takarar jam'iyyar
Demokrat mai mulki Hillary Clinton da kuma dan
takarar jam'iyyar adawa ta Refablika Donald
Trump bayan wani zazzafan yakin neman zaben
da aka jima ba a ga irinsa ba.
An soma jefa kuri'ar ne a kauyen Dixville Notch
na jihar New Hamshire da misalin karfe biyar
agogon GMT.
Sai dai tuni Amurkawa miliyan 46 suka jefa
kuri'unsu a jihohin da suka bude rumfunan
zabensu kwanakki gabanin wannan ranar ta
zaben gama-gari.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Amurkawa na zaben shugaban kasa na gaba"

Post a Comment