Zamfara: 'An kashe mutane 40 a wata mahakar zinari'

Rahotanni daga jihar Zamfara sun ce kusan
mutane arba'in ne aka kashe a cikin wani hari
da wasu 'yan bindiga suka kai kan wata mahakar
Zinari.
Haka ma wasu mutane da dama sun bata yayin
da wasu suka tsira da munanan raunukka a cikin
harin da aka kai ranar Litinin kan mahakar zinarin
wadda ke daura da kauyen Bindim na karamar
hukumar Maru.
Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa harin
ya zo bayan da 'yan bindigar wadanda ake zaton
'yan fashin shanu ne suka kwashe makonni suna
satar mutane don neman kudin fansa.
''Yawancin wadanda suka mutun lebarori ne
masu aikin hakar zinari da kuma wadanda suka
zo saye.'' In ji wani mazauni yankin, kodayake
kawo yanzu hukumomin tsaro a jihar ba su
tabbatar da faruwar lamarin ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Zamfara: 'An kashe mutane 40 a wata mahakar zinari'"

Post a Comment