Dakarun Kurdawa sun kutsa garin Bashiqa dake hannun IS

Dakarun Kurdawan Iraqi sun kutsa kai cikin garin
Bashiqa wanda mayakan IS ke rike da iko dake
arewa maso gabashin birnin Mosul.
Hayaki ya rika tashi sama lokacin da ake
arangama tsakanin dakarun Peshmerga da na
kungiyar IS a garin na Bashiqa.
Da safiyar Litinin ne daruruwan mayakan
Peshmerga da ke samun goyon hare-haren
dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta ta
sama, sun kara dannawa cikin garin daga
kusurwowi uku.
Rundunar sojin Iraqi ta ce ta gano wani wagegen
kabari da aka cika da gawarwakin mutane 100 a
kudancin birnin Mosul.
An haka kabarin ne a harabar makarantar koyon
ayyukan gona dake wajen garin Hamam al-Alil,
da dakarun suka shiga a cikin karshen mako.
A shekarar 2014, mayakan sun kai hari kan
kananan kabilu da jami'an tsaro a yankin, lokacin
da suka kutsa ta cikin arewacin Iraqi bayan da
suka karbe iko da birnin Mosul.
Majalisar Dinkin Duniya ta samu rahoton cewa
masu tada kayar bayan sun yi ta tafka ta'asa tun
lokacin da gwamnatin Iraqi ta fara yunkurin sake
kwato birnin na Mosul makonni uku da suka
gabata.
An yi zargin cewa a ranar 29 ga watan Oktoba
sun hallaka tsoffin sojoji na yakunan Hamam al-
Alili da Shura su 40, kana suka jefa
gawarwakinsu cikin kogin Tigris.
Akwai kuma bayanan da suka nuna cewa
mayakan na IS sun haka hanyoyin karkashin kasa
da dama a fadin garin na Bashiqa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dakarun Kurdawa sun kutsa garin Bashiqa dake hannun IS"

Post a Comment