An kai samame a Samsung kan zargin cin hanci a Korea ta Kudu

Masu gabatar da kara na kasar Korea ta Kudu
sun kai samame a ofisoshin kayan lataroni na
kamfanin Samsung.
Masu gabatar da kara na kasar Korea ta Kudu
sun kai samame a ofisoshin kayan lataroni na
kamfanin Samsung, a wani bangare na bincike
kan badakalar siyasar da ta shafi shugaba Park
Geun-hye.
Masu gabatar da karar na gudanar da bincike kan
zargin cewa kamfanin na Samsung ya bai wa 'yar
Choi Soon-sil, aminiyar shugabar kasar wasu
kudade.
An zargi Ms Choi da amfani da abokantakar
wajen yin katsalandan a cikin siyasar kasar da
neman alfarmar kasuwaci.
Kamfanin na Samsung ya tabbatarwa da BBC
samamen, amma ya ce babu wani karin bayani
da zai kara yi a kai.
Shugaba Park ta nemi gafara kan alakar ta da
Ms Choi, amma tana fuskantar matsin lambar ta
yi murabus.
Cikin kwanaki kadan da suka gabata, dubban
mutane a Korea ta Kudun sun yi ta zanga-zanga
a Seoul babban birnin kasar, suna kira ga
shugaba Park ta yi murabus kan badakalar cin
hanci.
Ms Choi, wacce daddiyar aminiyar Ms Park ce,
diyar wani shahararen jagoran addinin gargajiya
ne Choi Tae-min, da ke da alakar kud- da-kud da
mahaifin Ms Park, kana ita kan ta shugaba Park
Chung-hee.
Ms Park ta kasance shugabar kasa ta farko
mace, lokacin da aka zabe ta a zaben da aka
gudanar a shekara ta 2012.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kai samame a Samsung kan zargin cin hanci a Korea ta Kudu"

Post a Comment