Masu tada kayar baya sun fasa bututun mai a Niger Delta

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce masu
tada kayar baya sun fasa wani bututun mai
mallakar jihar Delta a garin Warri.
Wasu masu gadi a Bututan man na kamfanin
Trans Forcados, sun sha da kyar bayan da
mayakan sa kan suka bude musu wuta, kamar
yadda Dickson Ogugu shugaban al'ummar Batan
ya shaida wa AFP.
Rahotanni daga kamfanin dilancin labaran ya ce
wani jami'in soja ya tabbatar da harin.
A makon da ya gabata an fasa bututun bayan
shugaba Muhammad Buhari ya gana da wakilan
kungiyar masu tada kayar baya na yankin Niger
Delta a wani yunkuri na kawo karshen rikicin
yankin.
Kungiyar dai ta bukaci gwamnati ta kashe
akasarin kudin da Najeriya ta ke samu daga mai
wajen magance matsalar talauci, kuma ta dauki
matakai wajen kawo karshen malalar mai da ke
lalata muhallan yankin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Masu tada kayar baya sun fasa bututun mai a Niger Delta"

Post a Comment