Ana zargin Neymar da Barcelona da zamba

Wani alkali a Spaniya ya ce ya kamata a
gabatar da Barcelona da Neymar gaban kotu,
kan zargin zamba, wata guda bayan da aka
janye karar da aka shigar tun farko.
A ranar Litinin wata gidauniya mai suna DIS ce
ta bukaci a sake sauraren karar, inda ta ce an yi
mata cogen a lokacin da Neymar ya koma
Barcelona daga Santos a shekarar 2013.
Gidauniyar ce ke kula da hakkin dan kwallon na
Brazil a harkar sauya kungiya.
Zargin da Neymar da iyayensa suka karyata,
wanda daga bisani aka kuma kori karar tun a
cikin watan Yuni.
A cikin watan Satumba, babbar kotun Spaniya
karkashin Alkali Jose de la Mata ya bayar da
umarnin da a sake sauraren karar.
Dan wasan ya tsawaita zamansa a Barcelona
kan yarjejeniyar shekara biyar a cikin watan
Oktoba.
Tun a baya an umarci Barcelona ta biya tarar
kudi fam miliyan 4.7, saboda kokarin kauce wa
biyan haraji kan cinikin Neymar.
An bai wa masu shigar da kara na Spaniya
kwanaki 10 da su shirya gabatar da Barcelona da
Neymar gaban kuliya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ana zargin Neymar da Barcelona da zamba"

Post a Comment