An yi zanga-zanga kan gwamnan da ya yi 'saɓo' a Indonesia

Dubban Musulmi ne suke yin zanga-zanga a
Indonesia, inda suke kira a hukunta gwamnan
birnin Jakarta saboda ya yi sabo.
Basuki Tjahja Purnama, wanda Kirista ne, shi ne
dan kabilar China na farko da ya zama gwamna a
kasar da mafi yawan mutanenta Musulmi ne.
Masu zanga-zangar sun taru a Masallacin Istiqlal
kuma daga nan suka nufi fadar shugaban kasar.
'Yan sanda sun daura damara domin tunkarar
yiwuwar barkewar rikicin addini.
A shekarar 1998, an yi zanga-zangar kin jinin
'yan China lamarin da ya kai ga kona kantuna da
gidaje da kuma sace kayayyakin 'yansu.
'Yan kabilar China su ne kusan kashi daya cikin
dari na al'umar Indonesia kimanin 250m.
Mr Purnama, wanda aka fi sani da "Ahok", na
shirin sake tsayawa takara a watan Fabrairu na
shekarar 2017.
Sai dai wasu Musulmi sun ce bai kamata ya
tsaya ba, suna masu cewa bai kamata wanda ba
Musulmi ba ya jagoranci Musulmi.
Sun kara da cewa bai kamata ya rika amfani da
ayoyin Al-Qur'ani wajen yakin neman zabe ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An yi zanga-zanga kan gwamnan da ya yi 'saɓo' a Indonesia"

Post a Comment