Rasha za ta ci gaba da luguden wuta a Syria

Rasha ta sanar da cewa za ta sanya ido akan
tsagaita wuta na sa'o'i goma sha biyu, dan bai
wa mayaka 'yan tawaye da fararen hula da
marasa lafiya damar ficewa daga birnin Aleppon
Syria.
Tun da fari 'yan tawayen sun yi watsi da tayin da
Rasha ta yi musu na ficewa daga birnin tsakanin
jiya alhamis da yau juma'a, sun kuma ci gaba da
kokarin kutsawa yankunan da gwamnatin Syria ta
yi wa kawanya a gabashin gundumar birnin
Aleppo.
Inda suka ci gaba da harba makaman roka da kai
hare-haren kunar bakin wake da ya hallaka
fararen hula da dama cikin kwanaki shida da
suka gabata.
Da yammacin yau ne ake sa ran jiragen yakin
Rasha da Syria za su ci gaba da luguden wuta a
yankunan da 'yan tawaye suke fakewa.
Yakin basasar Syria da aka dauki shekaru biyar
ana yi tun bayan juyin juya hali da guguwar
sauyin da ta kada a kasashen gabas ta tsakiya,
ya san an yi asarar rayukan dubban 'yan kasar,
wasu muliyoyi sun rasa muhallansu, ya yin da
wasu miliyoyin kuma suka tsere daga kasar.
A bangare guda kuma shugaba Basharul Assad
wanda manyan aminan sa irin su Rasha ke
marawa baya, ya kafe kai da fata ba zai sauka
daga kujerar sa ba kamar yadda 'yan tawaye da
kasashen yammacin duniya suka bukata.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Rasha za ta ci gaba da luguden wuta a Syria"

Post a Comment