Mourinho ya caccaki 'yan wasan Manchester United

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya
zargi 'yan wasansa da yin wasa irin na "sada
zumunta" bayan sun sha kashi a hannun
Fenerbahce.
United ta fadi zuwa mataki na uku a rukunin A
na gasar cin kofin Europa bayan Fenerbahce ta
doke su da ci 2-1 a Istanbul.
Yanzu dai kungiyar ta lashe wasa biyu ne kawai
cikin wasanni bakwai da ta buga na dukkan
gasar da take ciki.
Mourinho ya ce, "duk kungiyar da aka ci wasa
bayan minti biyu da shiga fili ba a shirye take ba,
kuma ba ta da alkibla".
United ta ci kwallaye biyu kawai a wasanni hudu
na baya-bayan nan da ta buga, yayin da Chelsea
ta zura mata kwallo dakika 30 da soma wasa,
kuma Fenerbahce ta ci ta a dakika 65 na farko.
Moussa Sow ya fara zura kwallo, yayin da
Jeremain Lens ya kara ta biyu daga bangaren
Fenerbahce, kafin Wayne Rooney ya ci wa United
tata kwallon daga bisani.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mourinho ya caccaki 'yan wasan Manchester United"

Post a Comment