Ana ci gaba da kama wasu 'yan jarida a Turkiyya

An kama 'yan jarida tara da ke aiki da jaridar
'yan hamayya ta Cumhuriyet da ke Turkiyya,
kana aka tsare su a gidan yari kafin a yi musu
shari'a a birnin Istanbul.
Editan jaridar da mai zayyana hotunan barkwanci
da kuma wani mai rubuta sharhin da ke sukar
gwamnati na cikin 'yan jaridar da aka kama.
Su ne 'yan jarida na baya bayan nan da aka
kama ana zargi da sukar Shugaba Recep Tayyip
Erdogan.
Ranar Juma'a, an daure 'yan siyasa tara, cikin su
har da shugabannin jam'iyyar da ke goyon bayan
Kurdawa ta HDP.
Haka kuma ranar Asabar an kama 'yan jam'iyyar
HDP tara, cikinsu har da shugabannin yankunan
da suka hada da na lardin kudu maso gabashin
kasar na Adana.
Cumhuriyet na cikin tsirarun jaridun da suka rage
da ke ci gaba da sukar Mr Erdogan.
Ana zargin ma'aikatanta da alaka da fitaccen
Malamin nan dan kasar Fethullah Gulen da ke
zaune a Amurka, wanda ake zargi da hannu a
kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan
Yuli.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ana ci gaba da kama wasu 'yan jarida a Turkiyya"

Post a Comment