Sojoji sun sake 'ceto' wata 'yar Chibok

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun
sake samun daya daga cikin matan Chibok da
aka sace tun a shekarar 2014.
Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa ta
kasar, Kanar Sani Usman Kukasheka ya aikewa
manema labarai ta ce an gano 'yar Chibok din ce
a Pulka da ke jihar Borno lokacin da sojoji ke
tantance wasu daga cikin mutanen da suka
kubuta daga hannun 'yan Boko Haram daga dajin
Sambisa.
Ya ce sunan ta Maryam Ali Maiyanga, kuma tana
dauke da jariri dan wata goma mai suna Ali.
Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriyar ya ce
an mika ta ga likitoci domin su duba lafiyarta.
A watan Oktoba ne dai aka saki 'yan matan
Chibok 21 daga cikin 217 da ke hannun kungiyar
ta Boko Haram.
A wancan lokacin, kakakin shugaban Najeriya,
Malam Garba Shehu, ya ce "An sako matan ne
bayan tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati
da Boko Haram sakamakon shiga tsakanin da
gwamnatin Switzeland da kungiyar International
Red Cross suka yi."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Sojoji sun sake 'ceto' wata 'yar Chibok"

Post a Comment