Amurka: Ko wa ye zai yi nasara tsakanin Clinton da Trump?

'Yan takarar shugabancin Amurka na Hillary
Clinton da Donald Trump na gab da kammala
yakin neman zabe a jihohin da babu wanda kai
tsaye zai ce zai lashe kuri'un su.
Hasashe na baya-bayan nan ya nuna Misis
Clinton ce ke sahun gaba a yakin da ake yi na
shiga fadar White House, inda ta kai ziyara
yankunan da a makonni biyun da suka wuce ake
zaton za ta kai labari.
Wakiliyar BBC ta ce dukkan bangarorin biyu sun
zage dantse dan ganin sun yi nasara a zaben da
ke tafe a mako mai kamawa.
Misis Clinton dai ta ta marawa fitaccen mawakin
nan bakar fata Jay-Z baya a jihar Ohio dan
karfafawa Amurkawa bakar fata gwiwar fitowa
don kada kuri'a.
A bangare guda kuma hannayen jarin wasu
kamfanonin sun yi matukar faduwa, saboda
fargabar da ake kan cewa watakil Donald Trump
ne zai yi nasara a zaben da za yi cikin mako mai
zuwa.
Hannayen jarin kamfanin S&P sun fadi da kusan
kashi 4 cikin 100, amma farashin gwal ya samu
tagomashi fiye da makonnin da suka wuce.
Wakilin BBC ya ce masu zuba jarin na fargabar
ba su san irin tsarin da Mista Trump zai zo da
shi ba matukar ya zama shugaban Amurka.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Amurka: Ko wa ye zai yi nasara tsakanin Clinton da Trump?"

Post a Comment