Ana san ran Shugaba Buhari zai kara albashi na ma’aikata

Kungiyar Kwadago ta kasa na san Shugaban
Kasa zai kara albashin ma’aikatan kasar
– Watakila shugaban kasar ya kara yawan
albashin ma’aikatan idan ya zauna da
Kungiyar Kwadago ta kasa
– Ana sa ran Shugaba Buhari ya maida mafi
karancin albashin ma’aikata N56,000

Ana san ran Shugaba Buhari zai kara albashi
na ma’aikata bayan ya gana da Kungiyar
Kwadago ta Kasa watau NLC. Shugaban
wani bangare na NLC din ya tabbatar da
cewa Kungiyar za ta gana da Shugaba
Buhari domin tattaunawa game da batun.
Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa watau
NLC, Ayuba Wabba ya bayyana cewa NLC za
ta zauna da Shugaban Kasa Muhammadu
Buhari a yau. Shugaban Kasa Muhammadu
Buhari zai gana da Kungiyar Kwadago ta
Kasa NLC, da kuma Kungiyar ‘Yan Kasuwan
Najeriya watau TUC.
Ayuba Wabba, Shugaban wani bangare na
Kungiyar NLC yace sun gabatar da rokon su
ga Shugaba Buhari, ana kuma sa ran ya
duba wannan batu. Jaridar Daily Times ta
rahoto cewa Kungiyar Kwadago na kokarin
ganin an maida albashin ma’aikata ya kai
akalla N56000 a kowane wata.
Kungiyar Kwadago ta Kasa da kuma
Kungiyar ‘Yan Kasuwan Najeriya watau
TUC.sun gana a tsakanin su a Ranar Litinin,
kafin su je su samu Shugaba Buhari domin
fara zama. A yanzu dai mafi karancin
albashin ma’aikatan tarayya a Kasar shine
N18000, wanda tun lokacin Shugaba
Jonathan aka sama hannu. Ana neman
Shugaba Buhari ya kara albashin ma’aikata
zuwa akalla N56000 a kowane wata.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ana san ran Shugaba Buhari zai kara albashi na ma’aikata"

Post a Comment