FA ta hukunta Jose Mourinho

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta hukunta
kociyan Manchester United, Jose Mourinho, inda
ta ce ba zai ja ragamar kungiyar ba a wasa
daya.
Hukumar ta yanke wannan hukuncin ne, bayan
da alkalin wasa Mark Clattenburg ya bai wa
kociyan jan kati a karawar da United ta tashi
wasa babu ci da Burnley a gasar Premier.
Hukumar ta kuma ci kociyan tarar kudi fam
8,000, haka kuma wasan da United za ta yi da
Swansea ne hukuncin zai yi aiki a kansa.
Haka kuma hukumar ta ci tarar Mourinho kudi
fam 50,000 kan batun da ya yi a kan nada alkalin
wasa Anthony Taylor.
Mourinho ya ce nada Taylor a matsayin wanda
ya hura karawar da suka yi da Liverpool a Anfield
an sa shi cikin matsi.
A bisa doka ba a yadda mai horar da kwallon
kafa ya yi jawabi kan alkalin tamaula kafin a
buga wasa ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "FA ta hukunta Jose Mourinho"

Post a Comment