Ana zargin dakarun Iraq da kashe kauyawa

Kungiyar Amnesty International ta ce wasu maza
da suka sanya kaya irin na 'yan sanda sun
azabtar da mutane sannan suka kashe su a wasu
kauyuka da ke kusa da Mosul.
Shaidun da kungiyar ta tattaro sun nuna cewa an
harbe har lahira mutum shida a kauyukan Shura
da Qayyarah bayan an kulle su a kan zargin suna
da alaka da kungiyar IS.
Har yanzu hukumomi a kasar ba su komai a kan
batun ba.
A watan jiya ne dakarun da ke goyon bayan
gwamnatin kasar suka kaddamar da hare-hare na
sake kwace Mosul daga hannun mayakan IS.
Jami'an tsaro kusan 50,000 - cikin su har da
sojoji da 'yan sanda da mayakan Kurdawa na
Peshmerga da Larabawa mabiya Sunna da 'yan
Shia - na cikin wadanda ke fafatawa domin
kawar da IS daga birnin.
Jami'an Amnesty sun ziyarci yankuna da dama
domin ganin irin kisan gillar da ake zargin an yi
wa mutane bayan mayakan IS sun janye daga
yankunan, inda suka fitar da daruruwan mata da
kananan yara da tsofaffi, wadanda a fili take
cewa IS ta yi amfani da su ne a matsayin
garkuwa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ana zargin dakarun Iraq da kashe kauyawa"

Post a Comment