Dubban mutane sun yi zanga-zangar kyamar Trump

Dubban masu zanga-zanga ne suka fantsama a
kan titunan manyan biranen Amurka domin yin
adawa da zaben Donald Trump.
Da dama daga cikin su sun rika yin ihu suna
cewa "ba shi ne shugabanmu ba".
Wasu kuma sun rike mutum-mutumin Trump.
Mr Trump zai zama shugaban Amurka na 45
bayan ya lashe zaben da ya bai wa miliyoyin
mutane mamaki inda ya doke Hillary Clinton.
Nan gaba ne zai gana da Shugaba Barack
Obama a fadar White House domin tattaunawa
kan yadda za a mika masa mulki.
Mr Obama - wanda ya ce Mr Trump bai
"cancanta" ya zama shugaban kasar ba sannan
ya yi yakin neman kada a zabe shi - ya yi kira ga
dukkan Amurkawa su karbi sakamakon zaben
kamar yadda ya zo musu.
Ita ma Mrs Clinton ta shaida wa magoya bayanta
su bai wa Trump damar jagorantarsu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dubban mutane sun yi zanga-zangar kyamar Trump"

Post a Comment