Tsarin tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (2)

Marhala ta uku ta samu ne sanadiyyar
bayyana da yaduwar hanyoyi da na’urorin
sadarwa na zamani. Wannan, kamar sauran
dalilan baya, shi ma ya haifar da samuwar
kasashe da manyan kamfanonin sadarwa na
duniya wajen bisne manyan wayoyin sadarwa na
zamani masu suna “Fiber Optics,” don samar da
tsarin sadarwa mai inganci tsakanin nahiyoyin
duniya baki daya.
Wadannan wayoyi, sabanin wadanda suka gabace
su, suna iya taskance rubutattun bayanai ne, da
sauti/murya, da hoto mai motsi, da hoto mara
motsi, tare da bayanansu (Metadata), daga asali
zuwa tikewarsu (daga inda aka aika su zuwa
inda za a karbe su). Dukkan tekunan duniya a
makare suke da ire-iren wadannan nau’ukan
wayoyin sadarwa da ake bisnewa don jona
sauran bangarorin duniya da bayanai.
A bangaren tekun Atlantika ma haka lamarin
yake. Cikin shekarar 1920 aka fara yunkurin
bisne wayoyin sadarwa a karkashin wannan teku,
amma sai abin bai cinma nasara ba. Hakan ya
faru ne sanadiyyar rashin ingantacciyar fasahar
da za ta iya sawwake aikin, da kuma matsalar
tattalin arzikin kasa da duniya ta samu kanta
cikin shekarar 1930, wato: “Great Depression.”
Wannan ya sa sai cikin shekarar 1942 tukun
hakan ya yiwu.
Kamfanin “Siemens Brothers” mai reshe a birnin
Landan, ta hadin gwiwa da hukumar Burtaniya
mai suna: “British National Physical Laboratory,”
suka fara shimfida bututu a karkashin tekun
Atlantika. Sun yi haka ne don samar da bututun
mai na karkashin, wanda shi ne na farko a duniya
baki daya. Hakan ya faru ne a daidai lokacin
Yakin Duniya na II (tsakanin 1940 zuwa 1945
kenan).
Bayan kamfanin “Siemens” sai “Transatlantic-1”,
wanda shi ne kamfanin farko da ya fara bisne
wayoyin sadarwa na tarho a karkashin tekun
Atlantika. Kada a mance, kamfanin “Siemens” ya
bisne bututun mai ne, wanda shi ne na farko a
wannan bangare. Amma a babin sadarwa,
kamfanin “TAT-1” kamar yadda aka saba kiransa
a gajarce, shi ne na farko. Ya yi wannan aiki ne
tsakanin shekarun 1955 zuwa 1956, a daidai
gabar tsibirin Gallanach da ke kasar Scotland, da
gabar tsibirin Clanrebille dake Newfoundland a
kasar Kanada. Wadannan wayoyi na aika
bayanan murya ne da sauti, kuma suna dauke ne
da tashoshin tarho guda 36.
Haka lamarin ya ci gaba har zuwa lokacin da
fasahar Intanet ta bayyana, aka samu ci gaba a
fannin kere-keren lantarki. A daidai wannan
lokaci ne, sanadiyyar habbakar kimiyya da
fasahar sadarwa, bukata ta karu kan ingancin
tsarin sadarwa. Wannan ya samar da nau’ukan
na’urorin safaran bayanai daban-daban, ciki har
da wayoyin kebul nau’in “Fiber Optics.” Idan mai
karatu bai mance ba, a shekarar 2010 ko kasa da
haka kadan ne muka gabatar da kasidu wajen
hudu kan wannan fasaha, masu take: “Fasahar
Fiber Optics.”
Wannan fasaha ta wayoyin sadarwa nau’in waya
ce da aka kera ta daga damammen kunun
gilasai, aka daskarar da ita, sannan aka yanka ta
sille-sille. Babbar manufar hakan kuwa shi ne
don tabbtar da inganci wajen sadarwa da yawa
ko girman mizanin sakonnin da ake son wannan
fasaha ta rika dauka yayin aikawa da sakonni.
Idan mai karatu na son ya gane hakan, ya dauki
gilashi mai dan tsawo, a cikin duhu, ya haska
tocila daga farkonsa zuwa karshe; idan har ya
iya tantance tsawon lokacin da hasken ya dauka
tsakanin lokacin haskawa da isan hasken zuwa
karshen gilashin, to, wannan ita ce tazarar da za
ta dauka idan aka cillo siginar bayanan sadarwa
daga asali zuwa muntaha.
Kusan dukkan kamfanonin sadarwa na zamani
suna da manyan wayoyin sadarwa da suka bisne
a karkashin tekunan duniya, ciki har da tekun
Atlantika. Wannan gasa ce suke yi a tsakaninsu.
Kamfanin Yahoo!, da Microsoft, da Google, da
AT&T, da berizon da sauransu, duk suna da
wannan tsari.
Matsaloli
Babbar matsalar da ire-iren wadannan tsare-tsare
ke fuskanta, duk da ingancinsu wajen sadarwa da
samar da fa’ida ta kasuwanci, shi ne irin
hadarurrukan dake samuwa a tekun; ya Allah a
karkashi ne ko a saman tekun, wanda ke
gangarawa zuwa inda wadannan wayoyi suke.
Wadannan hadarurruka dai sun hada da girgizan
kasa da aman dutse da ake samu a karkashin
teku, wato: “Earthkuarke and bolcanic
Eruption.” Samuwar wannan yanayi na
sanadiyyar konewa ko yayyankewar wadannan
wayoyi. Sai kuma matsalar rubewa da
sanadiyyar tsawon zamani, musamman ga
wadanda aka binne su da jimawa.
Bayan haka, akwai matsalar dabbobin ruwa,
wadanda ke kokarin yagalgala wadannan wayoyi,
ko ta hanyar ci ko sarkafe jikinsu da su. Ba da
dadewa ba kamfanin Google ya sanar da cewa
lallai ya gano cewa manyan kifayen karkashin
teku (Sharks/Whales) na guiguyar wayoyinsa da
ya shimfide a karkashin tekun. Wannan, a
cewarsa, ba karamin hatsari bane ga bayanan da
wadannan wayoyi ke dauke da su. Amma ya
tabbatar da cewa ya samar da wata sabuwar
fasaha ta nau’in waya mai suna: “Kelbar,” wacce
ke da inganci, mai jure matsaloli irin wannan.
Wannan fasaha ta “Kelbar” dai nau’in waya ce
amma mai kama da tayar mota, wato wajen
dabi’a kenan, ba wai siffa ba.
Wannan, a takaice, na cikin gudunmawar tekun
Atlantika ga tattalin arzikin duniya da fannin
sadarwa, musamman nahiyoyin dake
makwabtaka da shi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Tsarin tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (2)"

Post a Comment