Arewa da sauran gyara

Arewacin Najeriya ita ce mafi girma, da
fadin kasa da kuma yawan jama’a, sai dai
ita ce koma baya ta fuskar ilimi da tattlin
arziki, sai dai a lokacin da kudu ke murnar
sabbin jami’oi, mu kuwa a arewa
manayanmu na bikin shekarau goma da
sarautar a cewar Shehun Malami Ahmad
Gummi
bikin hawan Durbar a Sokotio har da
Obasanjo
Dakta Ahmad Abubakar Gumi ne ya turo da
wannan sakon ta dandalin sada zumunta da
muhawara na Face book ya ce babu wata
murna da bangaren arewacin Najeriya zai yi
domin har yanzu akwai abubuwa masu
muhimmanci da ya kamata yankin ya cimma,
amna har yanzu sai tafiyar hawainiya yankin
ke yi.
Shehun Malamin na magana ne a kan yadda
manya sarakuna da masu fada a ji a suka
taru a Sokoto wajen bikin cika shekari 10 da
hawan alfarma Abubakar Sa’ad sarautar mai
Sarkin Musulmi bayan yankin ya fi kowanne
ci baya a Najeriya.
Wanna tsokaci ya zo ne a daidai lokacin da
shugaba Buhari ya bayar izinin kafa
sababbin jami’oi masu zaman kansu guda 8
a kudancin kasar, amma mu a arewa na
murnar shekaru goma da a wani begere tutar
daular shehu.
Sannan kuma a cikin jamioi 61 kafin
wadannan sababbin, da a ka yi a yanzu,
guda tara ne kacal a arewa, 3 a Kwara, 1 a
Adamawa, 1 a Taraba, 1 Kogi, 1 a Nasarawa,
1 Benue, sannan kuma1 a Katsina duk da
cewa mune da mafi yawan al’umma.
A kowanne lokaci muna kalubalantar
mutanen da ba su dace ba ko kuma bayanan
da ba su da mahimmanci, a wannan bangare
da mu ke da yawan marasa aikin yi, ga
talauci, ta ina za’a yi murna?
Ya dai kamata a wayarwa da mutane kai a
kan irin halin da a ke ciki a yanzu a arewa,
amma ba sharholiya ba.
Gaskiyar magana akwai banbacin ilimi, da ci
gaban tattalin arziki da kuma masana’antu,
ko rashin wadannan za su iya janyo mana
rikice-rikice na ta’adanci a arewacin
Najeriya.
Saboda haka ‘yan ta’ada sun bada
mummunan taimako don lalacewar rayuwar
mutanen arewa, suna yin fada ne don biyan
bukatunsu kansu kawai, daga karshe ina mai
fatan Allah ya haskakamu gaba daya, ya
kuma sa mu farak daga barcin da muke yi.
Amin

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Arewa da sauran gyara"

Post a Comment