Gagarumar girgizar kasa ta abkawa New Zealand

Hukumar da ke sanya ido kan sauyin yanayi ta
Amurka ta ce wata girgizar kasa mai karfin 7.4
ta abka wa yankin Christchurch da ke New
Zealand.
Ma'aikatar tsaro ta gargadi mutanen da ke gabar
teku daga gabashin South Island su matsa daga
yankin saboda yiwuwar faruwar tsunami.
Har yanzu dai birnin na Christchurch bai gama
murmurewa daga girgizar kasar da ta abka masa
a shekarar 2011 ba, wacce ta yi sanadin
mutuwar akalla mutum 185 sannan ta lalata
tsakiyar birnin.
New Zealand dai tana yanki ne wanda ke da
saurin faduwar girgizar kasa da tsagewar kasa.
Rahotannin farko sun nuna cewa wasu gidaje a
garin Cheviot, kusa da tsakiyar wurin da girgizar
kasar ta faru, sun lalace.
Wani mazaunin Christchurch ya ce girgizar kasar
ce ta tashe su daga bacci, sakamakon rawar da
gidaje suka rika yi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Gagarumar girgizar kasa ta abkawa New Zealand"

Post a Comment