Buhari da shugabannin Afirka sun taya Trump Murna

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Donald
Trump, zababben shugaban Amurka murnar
nasar zaben da yayi mai cike da mamaki.
Muhammadu Buhari ya ce a madadin gwamnatin
Najeriya da mutanen kasar baki daya yana taya
mista Trump murna.
Shugaban ya kara da cewa yana sa ran yin aiki
tare da Donald Trump domin karfafa dangantakar
da ke tsakanin kasashen biyu.
Shi ma a na sa bangaren, shugaba Mahamadou
Issoufou na Nijar ya taya Donald murna.
Issoufou ya bayyana hakan ne a sakon da ya
wallafa a shafinsa na twitter.
Haka zalika shugaban Ghana, John Mahama, ya
wallafa sakon murna a shafinsa na twitter kamar
yadda shi ma Macky sall ya taya zabben
shugaban kasar Amurkar murna.
Shugaba Macky Sall ya ce a shirye Senegal take
ta cigaba da karfafar dangantakar da ke
tsakaninta da Amurka.
Shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo,
Joseph Kabila, ya ce Trump ya samu gagarumar
nasara kuma a shirye yake ya yi aiki da
zababben shugaban domin karfafa dangantaka
da kawance da ke tsakanin kasarsa da Amurka

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Buhari da shugabannin Afirka sun taya Trump Murna"

Post a Comment