Donald Trump ya ce zai bai wa Amurka muhimmanci

Mista Donald Trump, ya ce zai saka muradun
Amurka gaba da komai, amma zai yi adalci ga
kasashen da ke da sha'awar tafiya tare da
Amurka. Ya bayyan hakan ne a lokacin da ya ke
jawabinsa na murnar samun nasara, sabon
zababben shugaba na Amurka,
Trump ya kara da cewa ''Kowane Ba'amurke, zai
samu damar yin cikakken amfani da baiwar da
Allah ya yi masa. Mutane maza da mata da aka
mance da su, yanzu ba za a mance da su ba''
Dan takarar Shugabancin Amurka na jam'iyyar
Republican, Donald Trump, ne dai ya lashe zaben
kasar da aka yi ranar Talata.
Mista Trump ya lashe zaben ne bayan da ya
samu nasarar cinye kujerun wakilai sama da 270
a jihohi 50, a inda ya kayar da abokiyar
hamayyarsa Hillary Clinton.
Trump, wanda ya gabatar da jawabin amincewa
da yin nasara, ya ce Clinton ta kira wo shi a
wayar tarho inda ta taya shi muranr lashe zaben.
A cewarsa, zai mayar da hankali wajen ganin ya
sake gina Amurka, yana mai cewa muradin kasar
su zai sanya farko a kan komai.
Yadda Donald Trump ya samu nasarar
zama shugaban kasa
Yadda Trump ya doke Clinton
Waye zai lashe zaben Amurka
Ya kara da cewa zai yi aiki tukuru wurin hada
kan jama'ar kasar, sannan ya nemi hadin kan
wadanda suka yi adawa da shi.
Ya kuma sha alwashin ganin ya saka Amurka a
gaba a duk huldar da zai yi da kasashen waje.
Sai dai ya ce zai yi alaka mai kyau ta mutuntaka
da sauran kasashe.
Nasararsa ta zo da matukar mamaki saboda
dukkan kuri'un jin ra'ayin jama'a sun nuna
Clinton na bayansa.
Taswirar adadin kuri'un da Hilary Clinton ta
samu
Jam'iyyar Democrat
A daya bangaren kuma, jam'iyyar ta Republican
ta sake rike rinjayen da take da shi a majalisun
dattawa da na wakilan kasar.
Taswirar adadin kuri'un da Donald Trump
ya samu
Jam'iyyar Republican

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Donald Trump ya ce zai bai wa Amurka muhimmanci"

Post a Comment