Trump: Shin Soyinka zai yaga katinsa na zama a Amurka?

Tambayar da 'yan Najeriya ke yi bayan Donal
Trump ya lashe zaben shugaban Amurka ita ce:
Shin shahararren marubucin nan na Najeriya,
Wole Soyinka, zai yaga katinsa na shaidar zama
a Amurka (green card), kamar yadda ya sha
alwashin, idan Trump ya ci zabe?
A kwanan baya ne dai Mista Soyinka ya ce ba
lallai ba ne Trump ya ci zaben, a lokacin da yake
jawabi a jami'ar Oxford da ke Birtaniya.
Ya kara da cewa amma kuma idan har ya ci, to
abu na farko da zai fada shi ne "duk masu katin
shaidar zama a Amurka na green card sai sun
sake neman izini".
Jaridar Guardian ta ambato Soyinka yana cewa
"Ni ba zan jira wannan ba."
Ya kara da cewa "Da zarar sun sanar da nasarar
shi, zan yaga kati na da kai na, sannan na fara
tattara kayana".
Mista Soyinka dai Malami ne a cibiyar nazari a
kan harkokin Afirka da Amurka da ke jami'ar New
York.
Shi ne mutumin Afirka na farko da ya samu
lambar yabo na Nobel a kan rubutun adabi a
shekarar 1986.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Trump: Shin Soyinka zai yaga katinsa na zama a Amurka?"

Post a Comment