Ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin Atiku da El- rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya, Nasir El-
Rufai ya yi zargin cewa tsohon mataimakin
shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar yana yin
zagon-kasa ga gwamnatin Shugaba Muhammadu
Buhari.
El-Rufai na yin raddi ne ga a zargin da Atiku ya
yi masa na saba wa ka'idojin aikin gwamnati a
lokacin da yake rike da mukamai a gwamnatin
Olusegun Obasanjo, sannan ya ce ya yi masa
butulci.
A wata hira da Premium Times ta wallafa, Atiku
ya ce shi ya shigar da El-Rufai gwamnati har ya
zama minista, amma da shi "aka yi amfani wurin
zargina da cin hanci", abin da kotu ta wanke ni
daga baya.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar, gwamnan El-
Rufai ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa
sun dabaibaye Atiku, abin da ya sa yake tsoron
zuwa Amurka.
Ya ce kamata ya yi wa duniya bayani kan
rahoton binciken da wani kwamitin majalisar
dokokin Amurka ya yi kan yadda aka shigar da
fiye da $40m na kamfanin Siemens cikin kasar,
kuma aka sanya su a asusunsa da na daya daga
cikin matansa.
Amma ana sa bangaren Atiku ya ce babu
gaskiya a lamarin: "Wannan rashin adalci ne a
rinka zargin mutum ba tare da hujja ba".
Nasir El-Rufai ya ce, "Alhaji Atiku yana son yin
takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2019 shi
ya sa yake tunanin idan ya bata mana suna zai
kai gaci.
Jarabar da yake da ita ta son yin mulki ce ta
sanya ya goyi bayan 'yan majalisar dokokin da
suka yi wa jam'iyyarmu bore, wanda kuma hakan
ke ci gaba domin kawai nuna rashin da'a ga
shugaban kasa".
Gwamnan na jihar Kaduna ya kara da cewa ya
goyi bayan Shugaba Buhari a zaben da ya wuce
kuma zai ci gaba da goyon bayansa domin fitar
da Najeriya daga kangin da ta fada a ciki.
Tuni dai jam'iyyar APC ta fara daukar dumi
saboda wasu batutuwa da wasu ke alakanta wa
da kokarin neman iko a zabe mai zuwa na 2019.
Shi ma uban jam'iyyar Sanata Ahmed Bola
Tinubu ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda
abubuwa ke gudana.
Ba wannan ne karon farko da Atiku da El-Rufa'i
ke yin sa'insa ba, sai dai wasu na mamakin dalili
da kuma tasirin da hakan ka iya yi a fagen
siyasar kasar a wannan karon.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin Atiku da El- rufa'i"

Post a Comment