Trump ya ce babu matsala a cikin tawagarsa

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya
kare shirinsa na karbar mulki yayinda ake tsaka
da samun rashin jituwa a cikin tawagarsa.
Mista Trump, hamshakin mai hada-hadar gidaje
ne kuma sabon shiga ne a jam'yyar Republican
wanda ya yi nasarar ba-zata a kan Hillary
Clinton.
Tuni dai Trump ya maye gurbin gwamnan New
Jersey Chris Christies da zababben mataimaki
Mike Pence a matsayin shugaban kwamitin mika
mulki.
Kafafen yada labarai na Amurka sun ce an
tursasa wa manyan mambobin kwamitin mika
mulkin biyu, wandanda ke aiki kan tsaron barin
ayyukansu.
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce
surikin shi da kuma Jared Kushner wani mai ba
shi shawara wanda yake da kusanci da shi suna
da hannu a sauyin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Trump ya ce babu matsala a cikin tawagarsa"

Post a Comment