Dakarun Iraqi sun kwace garin Nimrud daga mayakan IS

Dakarun sojin Iraqi sun ce sun kwace birnin nan
mai dimbin tarihi na Nimrud, wanda ke hannun
mayakan IS shekara biyu da suka wuce.
A watan Maris na shekarar 2015, jami'ai da
masana tarihi sun yi tur da IS saboda rushe
birnin, wanda aka gina tun karni na 13, da ta yi.
Hukumar kula da tarihi ta majalisar dinkin duniya
ta bayana rusa birnin da cewa laifin yaki ne.
Kungiyar IS dai ta ce zuwa hubbare da kuma
gina mutum-mutumi bautar gunki ce, wadda ya
kamata a hana.
Birnin na Nimrud yana da nisan kilomita 30 daga
birnin Mosul, wanda dakarun sojin na Iraqi suka
kaddamar da hare-hare domin sake kwace shi
tun a watan jiya.
Wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar ta
ce : "Dakarun runduna ta Tara sun kwato Nimrud
bakin daya kuma sun kafa tutar Iraqi a birnin
bayan sun karkashe mayakan IS."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dakarun Iraqi sun kwace garin Nimrud daga mayakan IS"

Post a Comment