Gerrard ya ce yana da zabin yin wasa a LA Galaxy

Tsohon dan kwallon Liverpool, Steven Gerrard,
ya ce yana da zabin lokacin da ya kamata ya
buga wasa ko kuma ya hutu, bayan da ya ce zai
bar LA Galaxy mai buga gasar Amurka.
Gerrard mai shekara 36, ya koma Galaxy a
shekarar 2015, ya kuma ci kwallaye biyar a
wasanni 34 da ya buga a kakar wasanni biyu.
Dan wasan ya ce zai bar Galaxy ne kwana daya
tsakani bayan da Frank Lampard ya ce ya kusa
ya bar kungiyar New York City wadda yake buga
wa wasanni.
Gerrard ya yi wa Liverpool wasanni 710 a
tsakanin 1998 zuwa 2015, kuma da zarar an rufe
kakar wasannin kwallon kafa ta Amurka, ya kan
yi atisaye ne a filin Melwood na Liverpool.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Gerrard ya ce yana da zabin yin wasa a LA Galaxy"

Post a Comment