Rikicin DRC: Jami'an MDD na ziyara a Beni

Wakilan kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin
Duniya na wata ziyara a yankin Beni da ke fama
da tashe-tashen hankali a gabashin Jamhoriyar
Dimukradiyar Congo, da nufin rage zaman dar-
dar a kasar.
Daruruwan fararen hula ne aka kashe a yankin na
Beni a cikin shekaru biyun da suka gabata.
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce an yi
biris da mutanen dake yankin.
A ranar Asabar, kwamitin tsaron na Majalisar
Dinkin Duniyan ya shaidawa shugaba Joseph
Kabila cewa, ya kamata ya mutunta kundin tsarin
mulkin kasar, ta hanyar sauka daga mulki idan
wa'adinshi na karshe ya kare a watan gobe.
An dage zabukan kasar, sannan an yi ta samun
tashe-tashen hankali a babban birnin kasar
Kinshasa da sauran wurare.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Rikicin DRC: Jami'an MDD na ziyara a Beni"

Post a Comment