EU zata kashe N50 biliyan wajen bangaren wuta a Najeriya

Gamayyar Turai (EU) zata saka jarin €150
miliyan wajen wuta a Najeriya
– Michael Arrion, jakada kuma shugaban
tawwagar gamayyar Turai ya fadi haka
– Za’a kuma horas da matasan injiniyoyi
FASHOLA
Michael Arrion, jakada kuma shugaban wata
tawwaga daga gamayyar Turai (EU) yace EU
zata kashe €150 miliyan (N50biliyan) kan ci
gaban wuta a Najeriya.
Ya fadi haka jiha 2 ga Nuwamba yayin da
yake magana a gefen taron tattaunawa na
biyar tsakanin EU da Najeriya kan kasuwanci
koko EU – Nigeria Business Forum (EUNIBF)
a Lagos. Arrion yace za’a yi amfani da mafi
yawan kudin wajen horas da injiniyoyi
matasa da kuma wasu aikace-aikace na
bangaren wuta.
Ya kuma ce EU na hada guiwa da
makarantar koyon aikin wuta ta kasa koko
National Power Training Institute (NAPTIN)
domin saka injiniyoyi matasa cikin sashen.
Ya ci gaba da bayyana muhimmancin saka
jari cikin harkar makamashi domin amfanar
tattalin arziki, yace babu abinda zai yi aiki
sosai idan ba’a saka isassun kudi a bangaren
ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "EU zata kashe N50 biliyan wajen bangaren wuta a Najeriya"

Post a Comment