Jason Brown na damuwa bayan ritaya

Kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa ta
Ingila (PFA), ta ce rayuwar 'yan wasan da suka
yi ritaya daga buga tamola daidai take da ta
tsofaffin sojoji , saboda yadda suke fafutuka da
rayuwa a karshen sana'ar tasu.
Kungiyar ta ce an samu karuwar kashi 25 cikin
dari na yawan 'yan wasan da suke neman
taimako kan matsalolin tabin hankali da damuwa
a shekarar da ta wuce.
Tsohon mai tsaron ragar Wales da kuma kungiyar
Gillingham da Aberdeen Jason Brown ya sheda
wa BBC yadda ya iya rayuwa da raunin da aka ji
masa a fuska da kuma kunnensa a lokacin
wasansa.
Amma yana ganin abu mafi wuya a wurinsa shi
ne, tunanin abubuwan da ya yi ba daidai ba da
kuma kudin da zai rika kashewa idan ya yi ritaya.
Tsohon golan ya ce, ''ba na barci, ba na cin
abinci. Tun ina dan shekara takwas ba abin da
nake yi sai kwallon kafa.
Sai kuma kawai wannan abu da nake yi, wato
wasan kwallon kafar ya bace ( ya zo karshe). To
yanzu na fahimci dalilin da ya sa mutane ke
kashe kansu.''

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Jason Brown na damuwa bayan ritaya"

Post a Comment