Wenger ya soki Fifa a kan Ingila da Scotland

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce Fifa, ba ta
yi daidai ba da ta hana 'yan wasa sanya kyallaye
masu alamar tunawa da sojin Burtaniya da na
Commonwealth da suka mutu a yakin duniya na
daya da sauran rikice-rikice, a wasan neman
shiga gasar kofin duniya da Ingila za ta yi da
Scotland.
Kocin na Arsenal ya ce, bai kamata Fifa ta shiga
wannan lamari ba, yana mai karin bayani da
cewa, wani lokaci idan kana son ka nuna cewa
daidai kake a kan akidarka ta siyasa, sai ka dan
saba wa al'ada.
Kocin ya ce, ''ina ganin wannan na daga al'adar
Ingila da nake kauna. Suna mutunta al'ada, kuma
suna martaba mutanen da suka sadaukar da
rayuwarsu ga kasar.''
Ita dai hukumar ta haramta sanya sakonnin
siyasa ko addini ko wata talla a jikin rigunan 'yan
wasa.
Ita dai wannan alama ana sanya ta ne a
makonnin kusa da kuma ranar 11 ga watan
Nuwamba, domin tunawa da sojin na Burtaniya
da na kungiyar kasashen renon Ingila da suka
mutu a yakin duniyar na daya da sauran yake-
yake da suka biyo baya.
Babbar Sakatariyar Fifa, Fatma Samba Diouf
Samoura za ta gana da ranar Alhamis din nan da
hukumomin kwallon kafa da ke Burtaniya a filin
wasa na Wembley, kuma mai yuwuwa su
tattauna a bayan fage kan batun in ji wakilin
BBC.
Samoura ta sheda wa BBC cewa, kowane irin
hukunci zai iya biyo baya, idan aka saba wannan
umarni na hukumar ta kwallon kafa ta duniya.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila, Martin
Glenn, ya gaya wa BBC cewa, 'yan wasan
bangarorin biyu za su yi watsi da wanna umarni
na Fifa, su sanya wannan jar alama, a matsayin
al'adarsu.
Ita ma hukumar kwallon kafa ta Scotland ta ce a
shirye take ta kalubalanci duk wani hukunci da
Fifa za ta yi wa 'yan wasanta kan daura kyalle a
hannuwansu, wato wannan alama.
A ranar Juma'a ta sama ne 11 ga watan
Nuwamba kungiyoyin na Ingila da Scotland za su
kara a wasan neman tikitin zuwa gasar cin kofin
duniya na 2018, a filin wasa na Wembley.
Fifa dai ta bar 'yan wasan Ingila da na Scotland
din sun sanya wannan alama da yanzu ake
wannan ja-in-ja a kanta, a kan bakin kyalle, suka
daura a hannuwansu, a lokacin wasan kasa da
kasa a watan Nuwamba na 2011.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Wenger ya soki Fifa a kan Ingila da Scotland"

Post a Comment